Aminiya awam
[search 0]
lebih
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Daga Laraba

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Mingguan
 
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa. A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan ma…
  continue reading
 
Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu…
  continue reading
 
Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa mak…
  continue reading
 
Dangantaka na kara runcabewa tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, wato Kano State Censorship Board, hukumar da aka kafa a shekarar 2001 domin kula da tsaftar fina-finai da nishaɗi a jihar, musamman a fannin kiyaye al’ada da koyarwar addini wacce daya daga cikin jaruman fina finan Abba El-Mustapha, ke jagoranta. A baya-bayan nan, hukumar …
  continue reading
 
Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni a ta yadda shugabanci zai rika kewaya a tsakanin shiyyoyi sh…
  continue reading
 
Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Daya daga cikin nau’ukan jarabawa da daliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Sharen Fagen Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma dalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB)…
  continue reading
 
Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa. Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa. Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba. Wannan ne batu…
  continue reading
 
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya. Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. Shirin Daga Laraba na wannan …
  continue reading
 
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan…
  continue reading
 
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. A kan wannan…
  continue reading
 
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken …
  continue reading
 
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin ma…
  continue reading
 
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar. Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari. Yayin da wasu suke …
  continue reading
 
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa. Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da …
  continue reading
 
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a k…
  continue reading
 
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son …
  continue reading
 
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan …
  continue reading
 
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta.…
  continue reading
 
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki. Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
  continue reading
 
Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samu…
  continue reading
 
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma. Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu. Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yad…
  continue reading
 
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su. Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su. Mene n…
  continue reading
 
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta m…
  continue reading
 
A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti. Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na …
  continue reading
 
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli. Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke adda…
  continue reading
 
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da al’ummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata. Duk da sauran ‘yan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takar…
  continue reading
 
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu. Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba. Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwat…
  continue reading
 
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan. Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe. Karancin jami’an tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jami’…
  continue reading
 
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya. A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata. Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga ya…
  continue reading
 
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan za…
  continue reading
 
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi. Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga gari…
  continue reading
 
Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a. Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa. Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya? Wannan ce muhawarar da ta…
  continue reading
 
Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara. Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar…
  continue reading
 
Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma. Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa. Shin me ya sa ake samun irin wannan? Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wa…
  continue reading
 
Sau da yawa akan samu rashin fahimtar juna a duk lokacin da wata mu’amala ta haɗa mata. Misali, a asibiti wajen haihuwa mata sun sha kokawa da yadda suke ce ’yan uwansu suna nuna musu rashin tausayi. Shirin Daga Laraba zai tattauna a kan wannan lamari, ya kuma auna shi a kan mizanin magamar da matan kan yi cewa “Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne”.…
  continue reading
 
Wata muhawara da ta karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita kasashen waje. Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan kudancin Najeriya suke wallafa fayafayen bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa kas…
  continue reading
 
Sama da mako guda ke nan bayan komawa makarantu domin fara sabon zangon karatu a kusan dukkanin sassan Najeriya. Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, ana samun karancin komawar dalibai makaranta a wasu sassan kasar. Shirin Daga Laraba na wananan makon zai yi duba ne a kan dalilan faruwar hakan.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
  continue reading
 
Dangantaka ko alaka a tsakanin Najeriya da China tana ƙara yaukaka, musamman a baya-bayan nan. Ko a kwanan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar ta China domin halartar taron kyautata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka. Shirin Daga Laraba na wananan mako zai tattauna a kan ko mecece ribar ’yan Najeriya…
  continue reading
 
A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu. Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a N…
  continue reading
 
Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum. Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare.…
  continue reading
 
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su. A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.…
  continue reading
 
A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna. A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya. To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin…
  continue reading
 
Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma. Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan in…
  continue reading
 
Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka. Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma. Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.…
  continue reading
 
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya. Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali. Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.…
  continue reading
 
Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi. A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri. Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuw…
  continue reading
 
Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa. A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine. Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.…
  continue reading
 
Loading …

Panduan Rujukan Pantas

Podcast Teratas
Dengar rancangan ini semasa anda meneroka
Main